Rashin fetur ya yi kamari a Ingila, an ga tsohon ‘Dan wasan Man Utd dauke da galan a kan titi

Rashin fetur ya yi kamari a Ingila, an ga tsohon ‘Dan wasan Man Utd dauke da galan a kan titi

  • Ana cigaba da fuskantar matsalar fetur a gidajen man da ke kasar Birtaniya
  • A cikin makon nan aka ga Paul Scholes yana rike da galan, zai cika motarsa
  • ‘Diyar tsohon ‘dan kwallon ta wallafa bidiyonsa ya karbi fetur a cikin galan

UK - Jaridar The Sun tace an hangi tsohon ‘dan wasan kwallon kafan Manchester United, Paul Scholes, yana dauke da galon yayin da ake fama da wahalar fetur.

Wata ‘diyar tauraron mai shekara 20 ta wallafa bidiyonsa a shafin Instagram yana rike da jarkar man fetur a gefen hanya a Ingila, yana kokarin cika tankin motarsa.

Rahoton yace Paul Scholes ya karbi man fetur a robar, da nufin ya samu na yawo a abin hawansa.

Da take yin tsokaci a kan shafin na ta na sada zumunta na Instagram. ‘diyar tsohon ‘dan kwallon na kasar Ingila ta tabbatar da yadda suka sha wahalar man a Ingila.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga

Alicia Scholes ta wallafa bidiyon a shafin Instagram a ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2021.

The Sun tace an ga tsohon ‘dan wasan tsakiyan yana sanye da bakaken tufafi. Wani mutumi ya miko masa mai a roba, shi kuma ya zazzage a tankin wata motarsa.

Gidan mai
Wani gidan mai a Ingila Hoto: www.kidsshop.top
Asali: UGC

Wani matakin ake dauka a UK?

Daily Trust tace ana fama da matsalar fetur a Birtaniya saboda karancin direbobin manyan motoci, hakan ya sa Firayim Minista ya dauki matakin gaggawa.

Shugaba Boris Johnson ya baza sojoji a Birtaniya da nufin kawo karshen wahalar man. Ba kasafai ne aka saba fuskantar irin wannan matsalar a kasar Turan ba.

Tuni dai gwamnati ta samu mutanen da aka fara koya wa tuka manyan motoci yayin da kimanin 90% na gidajen man da ke Birtaniya suke cigaba da zama a rufe.

Kara karanta wannan

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

Ana kyautata zaton cewa abubuwa za su dawo daidai, man ya samu a ko ina a karshen makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel